Rigimar APC: ‘Yan-a-mutun Adams Oshiomhole za su yi zama da Shugaban kasa

Rigimar APC: ‘Yan-a-mutun Adams Oshiomhole za su yi zama da Shugaban kasa

Rikicin APC ya kai inda ya kai a halin yanzu inda mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard cewa gwamnonin Imo, Osun da sauransu, sun fara kokarin ceton Adams Oshiomhole.

A makon da ya gabata ne Alkali ya dakatar da Adams Oshiomhole daga matsayin shugaban jam’iyyar APC. Wannan mataki na kotu ya raba kan ‘yan jam’iyyar zuwa gidaje biyu.

Gwamnonin da su ke kokarin zuwa fadar shugaban kasa domin ganin Adams Oshiomhole ya dawo kan kujerarsa sun hada da gwamnonin Kano, Borno, Osun, Legas da kuma Ogun.

Gwamna Abdullahi Ganduje Babagana Zulum, Adegboyega Oyetola, Babajide-Sanwo-Olu da Dapo Abiodun su na cikin wadanda ake ganin su na goyon bayan shugaban jam'iyya mai-ci.

Idan ba ku manta ba, jim kadan bayan dakatar da Oshiomhole, Shugaban gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi; da gwamnonin Jigawa da na Kebbi sun hadu da shugaban kasa Buhari.

KU KARANTA: Gaidom ya ce APC ta dawo hannunsa bayan dakatar da Oshiomhole

Rigimar APC: ‘Yan-a-mutun Adams Oshiomhole za su yi zama da Shugaban kasa

Wasu 'Yan APC sun rantse sai sun ga bayan Adams Oshiomhole
Source: UGC

Wani daga cikin ‘Yan majalisar NEC na jam’iyyar ya shaidawa Manema labarai cewa Ganduje, Zulum, Oyetola, Sanwo-Olu da Abiodun za su yi ta su ganawar a cikin makon nan.

Wadannan gwamnoni za su bukaci su yi wa shugaban kasa bayanin halin da ake ciki a jam’iyyar. Jigon jam’iyyar ya ce akwai bukatar shugaban kasa Buhari ya tsoma baki a rikicin.

Gwamnonin da ke kan gaba wajen ganin an bar Adams Oshiomhole a kan kujerara duk sababbin shiga ne, su ne: Farfesa Babagana Zulum, Hope Uzodinma da kuma Gboyega Oyetola.

Sauran gwamnonin jihohin Kano, Katsina, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Ogun da Yobe duk ba su tare da manyan Takwarorinsu masu neman ganin an yi waje da Kwamred Oshiomhole.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel