Tsaro da lantarki sun sa Jihohin Arewa maso Gabas za su gana a Jihar Gombe

Tsaro da lantarki sun sa Jihohin Arewa maso Gabas za su gana a Jihar Gombe

Mun samu labari a jiya cewa gwamnonin Arewa maso Gabashin Najeriya, za su yi wani taro a cikin jihar Gombe a Yau Alhamis, 5 ga Watan Maris, 2020.

Batun rashin tsaro ne babban abin da za a tattauna a wajen wannan taro kamar yadda Mai taimakawa gwamnan Gombe wajen yada labarai ya fada.

A Ranar Laraba, Mista Ismaila Misilli, ya fito ya sanar da cewa gwamnonin Arewa ta Gabas za su zauna a game da matsalar rashin tsaro da tattalin arziki.

Har ila yau, a wajen wannan taro na musamman da za ayi a Ranar Alhamis, gwamnonin jihohin za su tabo maganar hasken wutar lantarki da wasu batun.

Da ya ke jawabi a jiya, Ismaila Misilli ya ce taron na Ranar Alhamis, zai duba maganar danyen man fetur da aka samu a Yankin na Arewa maso Gabas.

KU KARANTA: Gwamnonin Jam'iyyar APC sun fara neman yadda za a sauke Oshiomhole

Tsaro da lantarki sun sa Jihohin Arewa maso Gabas za su gana a Jihar Gombe
Gwamnonin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe da Taraba za su zauna
Asali: Facebook

Gwamnonin Yankin za su duba yiwuwar su iya jan wutar lantarki da arzikin man. Gwamnonin jihohin za kuma su duba lamarin kamfanonin lantarki.

“Gwamnonin za su saurari jawabi game da damar da Yankin ya ke da shi daga bakin hukumar NEDC mai kula da cigaban Arewa ta Gabas.” Inji Misilli.

“A karshen wannan taro, gwamnonin za su fitar da matsaya da yarjejeniya da aka cin ma tsakanin wadannan jihohi shida na Arewa maso Gabas din”

"Wannan zama da za ayi yau shi zai zama na farko tsakanin gwamnonin Yankin, wanda zai zama kamar wani sharan fage domin kawowa shiyyar cigaba.”

Dazu kun ji cewa Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa, sun taya tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 83 a Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel