Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi, Bulama, Chukwuma a matsayin Shugabanni

Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi, Bulama, Chukwuma a matsayin Shugabanni

Jim kadan bayan kotu ta dakatar da Kwamred Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, majalisar NWC ta amince da wasu nadin mukamai.

Jam’iyyar APC ta nada sabon Sakataren jam’iyya na kasa da kuma Mataimakin shugaban APC na Yankin Kudancin Najeriya. An kuma nada sabon Mai binciken harkar kudi.

Wadannan shugabanni da aka nada a majalisar za su fara aiki ne a matsayin shugabannin rikon kwarya. Ana sa ran daga baya za a tabbatar da su a matsayin na din-din-din.

Kamar yadda mu ka samu labari, NWC ta nada Waziri Bulama ne a matsayin sabon Sakataren APC na kasa. Bulama zai maye gurbin da Gwamna Mai Mala Buni ya bari.

Haka zalika Abiola Ajiomobi ya shiga majalisar NWC a matsayin shugaban APC na Yankin Kudancin Najeriya. Tsohon gwamnan na Oyo ya canji wurin Niyi Adebayo.

KU KARANTA: Akwai yunkurin nada sabon Shugaba a Jam'iyyar APC - Majiya

Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi, Bulama, Chukwuma a matsayin Shugabanni

Abiola Ajimobi zai rike kujerar Shugaban APC a Kudu
Source: Twitter

Paul Chukwuma shi ne wanda aka nada a matsayin Mai binciken kudi na jam’iyyar APC. A shekarar bara, George Moghalu ne ya ke rike da wannan kujera a jam’iyyar.

Legit.ng ta samu labari cewa APC ta bada sanarwar nadin wadannan mukamai ne a Ranar Laraba, 4 ga Watan Maris, cikin dare. Lanre Issa-Onilu shi ne ya fitar da jawabi.

Sakataren yada labaran na jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa jam’iyyar ta cin ma wannan matsaya ne a wajen wani taro da ta yi a Watan Junarun 2020.

Sai dai wannan nade-nade da aka yi su na fuskantar kalubale inda wasu manyan APC ke nuna cewa ba a bi doka ba. A halin yanzu Victor Giadom ne Sakataren riko kwarya.

Arch. Waziri Bulama mai shekaru 58 ya fito ne daga jihar Borno. Shi kuma ya na cikin manyan APC a jihar Anambra. Abiola Ajiomobi ya sauka ne daga gwamna a 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel