Wata sabuwa:Masu suyar kosai za su fara biyan haraji a Kano

Wata sabuwa:Masu suyar kosai za su fara biyan haraji a Kano

- Masu gudanar da kananan sana’o'i da suka yi rumfa ko suka ajiye kwantaina a yankin karamar hukumar Birnin Kano da kewaye za su fara biyan wani tsarin haraji na kasa

- Wannan na kunshe ne a wata takardar da jami’ai suka dinga rarrabawa masu kwantainonin da rumfuna a unguwar Tukuntawa da ke karamar hukumar birnin

- A cewar takardar, duk wanda ya gaza biyan kudin wa’adin na kwanaki bakwai, karamar hukumar tana da ‘yancin daukar matakin a kansa

Masu gudanar da kananan sana’o'i da suka yi rumfa ko suka ajiye kwantaina a yankin karamar hukumar birnin Kano da kewaye za su fara biyan wani tsarin haraji na kasa mai suna “Temporary shed/stand permit”.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da jami’ai suka dinga rarrabawa masu kwantainonin da rumfuna a unguwar Tukuntawa da ke karamar hukumar birnin. Takardar ta nuna cewa mai kwantaina ko wanda ya yi rumfa yana sayar da kaya zai rika biyan kudi har naira dubu biyar cikin wa’adin kwanaki bakwai.

Wata sabuwa:Masu suyar kosai za su fara biyan haraji a Kano
Wata sabuwa:Masu suyar kosai za su fara biyan haraji a Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Satar waya: Kotun Najeriya ta yanke wa matashi Abdulkareem hukuncin kisa ta hanyar rataya

A cewar takardar, duk wanda ya gaza biyan kudin wa’adin na kwanaki bakwai, karamar hukumar tana da ‘yancin daukar matakin a kansa wanda zai kai ga rushe wajen sana’ar ta sa.

Wasu jami’an da ke raba takardar ga masu kwantainonin da rumfunan sun shaidawa gidan rediyon freedom na Kano cewa wannan umarnin daga karamar hukumar birnin Kano ta ke.

Toh amma kuma bayan ziyarar da gidan rediyon Freedom din ya kai wa sakateriyar karamar hukumar birnin don fayyace lamarin, jami’an sashin sun shaida cewa ba zasu iya cewa komai a kan hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel