Kudin diyar Ibro: Afakallah zai maka Baban Chinedu a kotu
Shugaban hukumar tace fina-finai da dabi’a ta jahar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba Afakallah, ya yi barazanar maka jarumin Kannywood kuma mawaki, Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu a gaban kotu, a kan ya yi masa kazafi da bata suna, Mujallar Fim ta ruwaito.
An tattaro cewa Baban Chinedu ya fitar da wani bidiyo a shafin sa na Facebook inda ya yi ikirarin cewa Afakallah ya cinye kudi har naira miliyan biyar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar domin a yi wa diyar marigayi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro) hidimar biki a lokacin da za a yi mata aure.
A bidiyon, har wa yau, Baban Chinedu ya nemi al'umma da su taimaka su shiga cikin lamarin domin a kwato wa iyalan Ibro hakkin su.
Ya kuma nemi malamai da su ma su shigo domin nema wa marayu hakkin su da ya ce wai Afakallah ya cinye.
Sai dai shugaban hukumar ya karyata zargin, inda ya umarci lauyoyin sa da su shigo cikin lamarin domin bi masa hakkin sa.
Har ila yau Mujallar Fim ta ruwaito cewa a takardar da lauyoyin su ka aike wa Baban Chinedu, sun bayyana cewa babu inda Gwamna ya ba Afakallah wannan kudi, sannan babu wani mutum da ya ba shi kuɗi don ya kai wa iyalan Ibro da har zai cinye.
KU KARANTA KUMA: Kannywood: A bar yi wa 'yan fim kudin goro - Khadija Yobe
Lauya Abdullahi Musa Karaye tare da abokan aikin sa lauyoyin da ke kare Afakallah sun umarci Baban Chinedu da ya sauke bidiyon da ya saka a dukkan shafukan sa na soshiyal midiya, sannan ya sake yin wani bidiyon na bayar da hakuri tare da karyata kan sa.
Daga karshe sun ba shi wa'adin awa 24 kacal ya yi hakan tare da gargadin cewa idan kuma ya ki yin wadannan abubuwan, to, kotu za ta dauki matakin da ya dace a kan sa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng