Jagororin APC sun koka da yadda ake gallaza masu a Jihar Zamfara

Jagororin APC sun koka da yadda ake gallaza masu a Jihar Zamfara

Mun samu labari cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Kwamred Adams Oshiomhole, ya yi tir da irin gallazawa Jagororin jam’iyyarsa da ake yi a Zamfara.

Adams Oshiomhole ya koka game da abin da ke faruwa ‘Ya ‘yan APC na reshen jihar Zamfara ne a lokacin da ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar na jihar a jiya.

Tsohon gwamna Abdulaziz Yari, shi ne wanda ya jagoranci ‘Yan APC na jiharsa zuwa gaban shugaban APC na kasa baki daya domin su gabatar da kukansu.

A cewar Adams Oshiomhole, jam’iyyar APC ta na kokari wajen kawo karshen halin da ‘Ya ‘yansa su ke ciki. Sannan ya kara kiransu da su jajirce a kan matsayarsu.

“Kamar yadda ku ke gani, zai iya yiwuwa yau ka na da mulki, gobe kuma ba kai ba ne. Dole doka ta yi aiki a kan kowa ba tare da nuna wani banbancin siyasa ba.”

KU KARANTA: Musulmai ba su amfana da mulkin Buhari ba – Inji Kukah

Jagororin APC sun koka da yadda ake gallaza masu a Jihar Zamfara
Manyan APC sun ce Gwamna Matawalle ya na gallaza masu
Asali: Facebook

”Dole kowa ya mallaki damar shiga cikin kungiya, da damar zuwa inda ake so, tare da bada damar mutum ya fadan abin da yake da ‘yanci.” Inji Oshiomhole.

Oshiomhole ya ce: “Ina murna duk da irin gallaza maku da ake yi da bankara doka domin cafke mutane a garkame su ba tare da hakki ba, ba ku karaya ba.”

“Ni na yi amanna za ka iya daure ni, amma ba za ka iya daure kaunar da na ke yi wa jam’iyyata ba, kuma muddin na sa rai a abu, sai inda karfi na ya kare."

“Ina so in gode maku na kawo zaman lafiya a jihar ta yadda ba ku dauki nauyi a hannunku.” A baya 'Yan APC sun koka da cewa gwamnan PDP ya taso su a gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel