Gwamnatin Tarayya ta na so Majalisa ta amince mata karbo bashin $22.8b

Gwamnatin Tarayya ta na so Majalisa ta amince mata karbo bashin $22.8b

Mun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dumfari majalisar dattawa da wani kokon bara na samun damar karbo bashin biliyoyin daloli daga kasar waje.

Ministar tattalin arziki da kasafin kudin Najeriya, Zainab Ahmed ce ta bayyana a gaban kwamitin harkar bashin gida da waje a Ranar Talata, 4 ga Watan Fubrairun 2020.

Misis Zainab Ahmed ta yi wa Sanatocin kasar bayani cewa an kasa inda za a karbo wannan bashi da ake nema zuwa gidaje bakwai a hannun manyan hukumomin Duniya.

Mai girma Ministar kudin ta kuma yi wa ‘Yan majalisar dattawan bayanin cewa wannan aron kudi da gwamnati ta ke nema ya na cikin tsare-tsarenta na 2016 zuwa 2018.

Ahmed ta kara da nunawa kwamitin majalisar cewa bashin zai yi aiki ne wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar gina abubuwan more rayuwa a fadin kasar.

KU KARANTA: Bashin da Najeriya ta ke karbowa ya fara yawa - CBN

Gwamnatin Tarayya ta na so Majalisa ta amince mata karbo bashin $22.8b
Ministar kudi ta ce Najeriya za ta iya biyan wannan bashi da ta ke ci
Asali: UGC

Haka zalika Ministar ta shaidawa Sanatoci cewa wadannan kudi za su yi amfani a wajen harkar noma da kuma bunkasa wutar lantarki, tare da yin aikin dogon jirgin kasa.

Bayan haka, idan aka karbo aron wannan kudi Dala biliyan 22.8, za a yi amfani da shi wajen taimakawa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da jarin da ake kira SME.

Wannan shiri na SME zai taimakawa Matasa da aikin yi a daidai lokacin da ake kukan rashin abin yi. Ministar ta ce Najeriya ta na da karfin biyan wannan bashi daga baya.

Ministar ta kara jaddada cewa bashin da ke kan Najeriya bai yi yawa ba, duk da kukan da wasu su ke yi. Ministar ta ce matsalar rashin kudin shiga ake fama ita a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng