K’anin Sultan, Bala Abubakar, ya sha kashi a zaben da aka yi a Jihar Sokoto

K’anin Sultan, Bala Abubakar, ya sha kashi a zaben da aka yi a Jihar Sokoto

A karshen makon da ya gabata ne hukumar zabe mai zamanta watau INEC, ta gudanar da wasu zabuka a Mazabu daban-daban a fadin Najeriya.

Daga cikin wuraren da aka shirya zabukan a Ranar Asabar, akwai jihar Sokoto inda jam’iyyar PDP da ke rike da jihar ta samu gagarumar nasara.

Mun samu labari daga Daily Trust cewa jam’iyyar PDP ta karbe kujerar Yankin Arewaci da Kudancin Sokoto a majalisar wakilan tarayya.

Abubakar Abdullahi wanda ya rikewa jam’iyyar PDP tuta shi ne wanda ya yi nasara a zaben. Wannan na nufin zai tafi majalisar wakilai.

Alhaji Abdullahi ya doke ‘Danuwan Sarkin Musulmi, Mai alfarma Sultan Muhammadu Sa’ad watau Honarabul Bala Hassan Abubakar III.

KU KARANTA: 'Dan Majalisan APC ya sauya-sheka zuwa PDP kafin ranar zabe

K’anin Sultan, Bala Abubakar, ya sha kashi a zaben da aka yi a Jihar Sokoto
Bala Abubakar ya bar kujerar Majalisar Tarayya a Sokoto
Asali: Twitter

Kafin wannan zabe Bala Hassan Abubakar III shi ne wanda ya ke kan kujerar Majalisar wakilai a yankin a karkashin jam’iyyar APC mai rinjaye.

Sakamakon zaben da aka fitar ya nuna cewa PDP ta samu kuri’a 68, 985. Bala Abubakar III na jam’iyyar APC kuma ya samu kuri’u 42, 433.

PDP ta ba APC ratar fiye da kuri’a 26, 000 a zaben kamar yadda Malamin zaben da ya yi aiki a madadin INEC, Mansur Ibrahim, ya bayyana.

Farfesa Ibrahim, kwararren Malamin ilmin shari’a ne a jami’ar tarayya ta Usman Danfodio ta Sokoto, shi ne ya sanar da sakamakon zaben.

Akwai kuri’u 5, 655 da aka yi watsi da su saboda kuskuren da aka yi wajen kada kuri’ar. PDP ta lashe wasu kujeru hudu a zaben da su ka gudana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel