EFCC ta zargi ‘Dan takara da amfani da kudi wajen sayen kuri’a a Imo

EFCC ta zargi ‘Dan takara da amfani da kudi wajen sayen kuri’a a Imo

Jami’an hukumar EFCC masu yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa sun kai samame a lokacin da ake gudanar da zabe a Jihar Imo a makon da ya gabata.

Kamar yadda mu ka samu labari, Ma’aikatan na EFCC sun ziyarci wata rumfar zabe ne da ke cikin Garin Isiala Mbano, bisa zargin cewa ana sayen kuri’un Talakawa.

A Ranar Asabar da ta wuce, 25 ga Watan Junairun 2020, aka gudanar da zaben kujerar ‘Dan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Mazabar Okigwe ta Arewa.

Ma’aikatan hukumar sun tsare ‘Dan takarar PDP, Obinna Onwubuariri, inda su ka yi masa tambayoyi game da zargin da ke kansa na amfani da kudi wajen zabe.

Ma’aikatan na EFCC sun shaidawa hukumar dillacin labarai cewa sun samu labarin ‘Dan takarar PDP kuma ‘Dan majalisa mai ci ya na rabawa masu kada kuri’a kudi.

KU KARANTA: Tambuwal ne sabon SHugaban Gwamnonin PDP a Najeriya

A lokacin da wannan abu ya faru Hon. Onwubuariri shi ne ‘Dan majalisa mai wakiltar Mutanen mazabar Okigwe da kewaye a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.

Kotu ta ruguza zaben da aka yi a Yankin a 2019 ne saboda irin wannan zargi na magudi da sabawa ka’idojin zabe, wannan ya sa aka bukaci a shirya danyen zabe.

A wannan zaben da aka yi, jam’iyyar PDP ta sha kashi a hannun APC. Wannan ya sa Obinna Onwubuariri ya rasa kujerarsa wajen wanda APC ta tsaida takara.

Mutane da-dama sun yi mamaki da jin labarin jami’an EFCC sun je rumfar zabe, Amma amfani da kudi wajen karkato da ra’ayin masu zabe babban laifi ne a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel