Rikicin sabbin masarautu: Yadda ta kaya a kotu a tsakanin dattijan Kano da Ganduje a ranar Litinin

Rikicin sabbin masarautu: Yadda ta kaya a kotu a tsakanin dattijan Kano da Ganduje a ranar Litinin

A yau Litinin ne wata babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 27 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar da dattijan jihar Kano suka shigar ta neman a dakatar da sabuwar dokar kirkirar sabbin masarautu guda hudu a Kano.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa dattijan Kano su 19 a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Usman Tofa sun shigar da kara a gaban kotu domin kalubalantar sabuwar dokar da ta bawa gwamnatin Kano damar kirkirar sabbin masarautu.

Wadanda sunansu ya bayyana a karar da dattijan suka shigar sune kamar haka; shugaban majalisar dokokin jihar Kano, alkalin alkalai na jihar Kano, Tafida Abubakar Ila (sarkin Rano), Ibrahim Abdulkadir Gaya (sarkin Gaya), Dakta Ibrahim Abubakar II (sarkin Karaye), Aminu Ado Bayero (sarkin Bichi), fadar Kano da sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.

Yayin zaman kotun, babban lauya A. B. Mahmoud, SAN, ya sanar da cewa an shigar da karar ne domin neman kotu ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da sauran kunshin sabbin dokokin masarautu da gwamnatin jihar ta kirkira.

Rikicin sabbin masarautu: Yadda ta kaya a kotu a tsakanin dattijan Kano da Ganduje a ranar Litinin
Alhaji Bashir Usman Tofa
Asali: Twitter

Lauyan dake kare wadanda kara kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Ibrahim Mukhtar, ya fada wa kotun cewa akwai bukatar karin lokaci kafin a fara sauraron karar saboda wasu daga cikin wadanda ake kara basu samu sanarwa ba sai da safiyar yau (Litinin), a saboda haka suna bukatar lokaci domin nazartar takardun karar da suka karba.

DUBA WANNAN: 'Ra'yinka bai dameni ba' - Buhari ya mayar wa da TY Danjuma martani

Lauoyi Yahaya Abdullahi da Ma'aruf Kasim dake kare kare dattijan Bichi da masarautar Rano sun bukaci a shigar da sunayensu a cikin wadanda ake kara domin sune zasu cigaba da wakiltar masarautar Bichi da Rano.

Jastis Nura Sagir ya ce kotun zata yi mahawara a kan bukatar da lauyoyin suka gabatar a zamanta na ranar 19 ga watan Maris.

Kazalika, ya daga ci gaba da sauraron karar da dattijan suka shigar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel