'Yan sanda sun kashe asurgumin dan bindiga, Yunusa Boka, da ya addabi kananan hukumomi 2 a Katsina
Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta kara kashe wani kasurgumin dan ta'adda, Yunusa Boka, wanda ya addabi kananan hukumomin Danmusa da Kankara.
Da yake tabbatar da harbe dan bindigarm kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katgsina, DSP Gambo Isah, ya ce jami'an 'yan sanda sun samu nasarar kashe dan bindigar ne a wani atisayen hadin gwuiwa da dakarun soji.
"A jiya (Talata) ne da misalin karfe 6:00 na yamma jami'an 'yan sanda da hadin gwuiwar sojoji suka kai hari sansanin masu garkuwa da mutane dake cikin surkukin dajin Gwarjo dake yankin karamar hukumar Matazu a nan jihar Katsina," a cewarsa.

Asali: Twitter
Isah ya ce, bayan musayar wuta ta tsawon lokaci da 'yan bindigar, jami'an tsaro sun samu nasarar kubutar da da wata mai jego da jaririnta mai wata bakwai da 'yan bindigar suka yi garkuwa dasu.
Asali: Legit.ng