Shehu Sani ya nemi EFCC ta biya shi miliyan 100 na tsare shi ba bisa ka’ida ba

Shehu Sani ya nemi EFCC ta biya shi miliyan 100 na tsare shi ba bisa ka’ida ba

Tsohon sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya ta takwas, Shehu Sani ya yi ikirarin cewa cigaba da tsare shi da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke yi ba tare da gurfanar dashi ba ya saba ma yancinsa, don haka yana neman ta biya shi naira miliyan 100 na barna.

Don haka, dan majalisar ya kai EFCC da Shugaban kamfanin AS Motors, Alhaji Sani Dauda wanda ya zarge shi da damfara, gaban babbar kotun tarayya, Abuja inda aka saurari shari’a akan take hakkinsa a ranar Litinin.

Mai ba Sani shawara na musamman, Suleiman Ahmed, jiya Talata, ya bayyana cewa shari’an ya gabata a kotu amma an dage shi zuwa ranar Laraba, 22 ga watan Janairu.

A karar da lauyan Sani, Abdul Ibrahim (SAN) ya gabatar a gaban kotu, ya yi ikirarin cewa tsare tsohon dan majalisar da EFCC ta yi “ba tare da kai shi kotu a cikin Abuja ba kuskure ne, baya bisa doka don haka an take masa yanci a karkashin sashi 35 (5) da (6) na kundin tsarin mulki.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta yi gargadi kan tashohin bincike na bogi a titin Maiduguri-Damaturu

Lauyan na so kotu ta hana wadanda ake kara daga damu, shiga zarraf, barazana ko take yancin wanda ke kara ta hanyar cigaba da barazanar gayyatarsa, kamawa, tsarewa, cin zarafi ko yi masa tambayoyi marasa tushe.

Ibrahim ya nemi a biya wanda yake karewa naira miliyan 100 a matsayin barna na take masa yancinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel