An kama wata matashiya, Zainab, tana kokarin sayar da jariri a Kano

An kama wata matashiya, Zainab, tana kokarin sayar da jariri a Kano

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta sanar da cewa ta kama wata matashiya, Zainab Adam, yayin da take kokarin sayar da jaririn data haifa ba tare da aure ba.

A cewar rundunar 'yan sanda, ta kama matashiyar, mai shekaru 25, yayin da take gararambar neman mai sayen jaririn.

Da yake holin Zainab tare da wasu masu laifi a hedikwatar 'yan sandan jihar Kano, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, ya ce sun kama matashiyar ne ranar daya ga watan Janairu a unguwar Giginyu dake cikin garin Kano.

DSP Haruna ya bayyana cewa Zainab, mazauniyar unguwar Hotoro, ta sanar da rundunar 'yan sanda cewa ta haifi jaririn ne ba tare da aure ba.

"A ranar daya ga wata ne jami'an rundunar 'Puff Adder' suka cafke wata matashiya mai suna Zainab yayin da take yawon neman wanda zai sayi jaririn data haifa. Jami'an mu sun kamata ne bayan samun bayanan sirri," a cewar DSP Haruna.

Sai dai, bai bayyana farashin da matashiyar zata sayar da jaririn nata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel