Masu garkuwa da mutane sun saki basaraken da suka sace a Kano

Masu garkuwa da mutane sun saki basaraken da suka sace a Kano

A ranar Alhamis ne dagacin garin Karshi dake karkashin karamar hukumar Rogo ya shaki iskar 'yanci bayan wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shi tun ranar Litinin.

An sace dagacin ne ranar Litini a garinsa na Karshi mai makwabtaka da jihar Kaduna ta kudancin jihar Kano.

Masarautar Karaye da rundunar 'yan sandan jihar Kano sun tabbatar da sace basarake a cikin sanarwa daban - daban da suka fitar.

Bayan sace Basaraken ne rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta sanar da cewa ta tura wata tawagar jami'anta na musamman domin kubutar da dagacin da kuma kama 'yan bindigar da suka yi awon gaba da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel