Yanzu Yanzu: Tambuwal ya yi umurnin biyan karancin albashi ba tare da bata lokaci ba

Yanzu Yanzu: Tambuwal ya yi umurnin biyan karancin albashi ba tare da bata lokaci ba

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal a ranar Juma’a, 10 ga watan Janairu ya yi umurnin fara biyan ma’aikata karancin albashi na 30,000 wanda aka aiwatar a jihar.

Tambuwal ya yi umurnin cewa a fara biyan ma’aikatan gwamnati sabon albashin daga lokacin biyan albashin watan Janairu 2020.

Gwamnan ya kuma bukaci a tantance ma’aikata ba tare da bata lokaci ba domin kakkabe ma’aikata na bogi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnan ya bayar da umurnin ne lokacin da ya karbi rahoton kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa kan aiwatar da sabon karancin albashi.

Tambuwal ya yi alkawarin biyan ma’aikatan albashin da suke bi sakamakon abunda ya kira a matsayin tsarin matakin ladabtarwa da gwamnatin jihar ta dauka.

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta fara binciken bidiyon 'dan sanda mai POS

Da sabon albashin nan ya ce yawan kudin albashin jihar zai koma naira miliyan 340 sabanin na baya da yake naira miliyan 324.

Gwamnan ya yaba ma jami’an kungiyar kwadago da na gwamnati kan kokari, dattaku da hakurin da suka nuna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel