Mayakan Boko Haram sun sace matafiya 7 a daf da Maiduguri

Mayakan Boko Haram sun sace matafiya 7 a daf da Maiduguri

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne sun yi kwanton bauna tare da yin awon gaba da matafiya 7 a kan titin Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Premiun Times ta rawaito cewa wani fasinja da ya sha da kyar, ya shaida mata cewa 'yan bindigar dake cikin motoci guda biyu kirar 'Hilux' sun datse hanya tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji dake cikin wata motar sufuri mallakar jihar Adamawa da kuma wata karamar motar kirar 'Volkswagen Golf'.

Majiyar ta ce dukkan 'yan bindigar na dauke da makamai, wasu kuma a cikinsu suna sanye da kakin sojoji.

A cewar shaidan, wanda ya nemi a boye sunansa, lamarin ya faru ne a garin Auno mai nisan kilimita 20 zuwa Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

"Sun zo ne a cikin wasu manyan motoci 'Hilux' guda biyu yayin da muke nufar kauyen Auno bayan mun bar kauyen Jakana. Wata mota kirar 'Volkswagen Golf' suka fara tsyar wa tare da umartar duk mutanen cikinta, har da direba, su fito," a cewar majiyar.

Shiadar ya cigaba da cewa, "ana cikin haka sai wata babbar motar fasinjoji mallakar 'Adamawa Sunshine' ta kawo kai wurin a cikin rashin sani. Sun tafi da fasinjoji guda biyu daga cikin motar tare da biyar na karamar motar farko."

"Tun da direbanmu ya hango motocin 'yan bindigar sai ya taka birki ya tsaya kasancewar bai fahimci abin da ke faruwa ba da farko. Amma bayan ganin an tsare mota ta biyu an umarci wasu fasinjojin su fito, sai ya saka giya, ya koma da baya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel