Gwamnati: Mun rufe gidan Marayun Du Merci ne saboda bai da rajista

Gwamnati: Mun rufe gidan Marayun Du Merci ne saboda bai da rajista

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ta rufe wani gidan Marayu mai suna Du Merci Orphanage Home wanda ya dade ya na aiki.

Mai ba gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje shawara a kan harkar jin dadi da walwalar yara da mata, Fatima Abdullahi Dala, ta bayyana haka.

Fatima Dala ta ke cewa: “An gano cewa wannan gidajen marayu wanda ya ke da takawara a Kaduna ya yi shekaru 25 ya na aiki babu lasisi.”

Honarabul Dala ta ce wadannan gidajen marayu sun shafe shekaru ne ba tare da sun samu takardar aiki daga gwamnatin Kano da Kaduna ba.

“Daga rahoton da mu ka samu daga wasikun da mu aikawa hukumomi, mun gano cewa gidan marayun bai da rajista.” Inji Mai bada shawarar.

KU KARANTA: Masarauta: Gwamnatin Ganduje da Dattawan Kano za su koma kotu

Gwamnati: Mun rufe gidan Marayun Du Merci ne saboda bai da rajista
An rufe Gidan Marayun Du Merci da ke Unguwar Sabon Garin Kano
Asali: Facebook

“Wannan babban laifi ne daga shugabannin da su ka kafa wannan gidan marayu da masu gudanar da harkokinsa, ace ya yi shekara 25 ya na aiki.”

Dala ta kuma ce: “Hakan ya jawo zargin ana aikata rashin gaskiya, wanda ya na iya zama laifi ga tsaron kananan yara da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar.”

Haka zalika gwamnatin jihar Kano ta kara da cewa bai kamata wasu su rika yi wa wannan aiki da aka yi kallon addini ko kabilanci da sauransu ba.

Hadimar gwamnar ta nemi jama’a su yi tir da wannan danyen aiki da aka dade ana yi, ta kuma godewa kokarin jami’an tsaro da hukumar NAPTIP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel