An kama dillalin bindigogi da aka dade ana nema ruwa a jallo a Legas

An kama dillalin bindigogi da aka dade ana nema ruwa a jallo a Legas

- Babban dillalin bindigogi na jihar Legas ya shiga hannun 'yan sanda a yankin Mafolokun dake Oshodi

- An cafke Samuel Uche ne a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu a hanyarsa ta zuwa siyar da wasu bindigogi

- 'Yan sandan sun ce Uche na cikin jerin mutanen da hukumar ta dade tana nema ruwa a jallo saboda sana'arsa

A ranar Laraba, 8 ga watan Janairu ne 'yan sanda suka kama wani dilan bindigogi mai shekaru 32 a duniya mai suna Samuel Uche, a yankin Mafolukun dake Oshodi a jihar Legas. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, runduna ta musamman mai kula da fashi da makami ce ta kama wanda ake zargin a kan hanyarsa ta zuwa siyar da wasu bindigogi biyu ga masu garkuwa da mutane da kuma 'yan fashi.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, yace Uche ya kasance cikin jerin mutanen da suke nema ruwa a jallo saboda zarginsa da suke da samar wa 'yan fashi da makami miyagun makamai. Odumosu yace sun bibiyi Uche ne kuma sun kama shi ne sakamakon bayanin sirri da 'yan sandan suka samu.

DUBA WANNAN: Shugaba Saleh na Iraqi ya soki harin makamai masu linzami da Iran ta kai

Kwamishinan 'yan sandan yace: "An ganshi da bakar leda, lamarin da yasa aka fara zarginsa. Sun bibiyesa kuma daga baya aka kama shi. A lokacin da aka binciki ledar, an samu bindigogi kanana guda biyu."

"A yayin da aka tuhumesa, ya bada sunansa da Samuel Uche kuma yana da shekaru 32. Ya tabbatar da cewa ya siyo bindigogin ne don zai siyar wa wani gungun 'yan fashi da makami tare da wasu masu garkuwa da mutane a kan N250,000," Odumosu yace.

Ya kara da cewa za a mika wanda ake zargin gaban kuliya bayan an kammala bincike..

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel