Shugaban kasa Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Mele Kyari

Shugaban kasa Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Mele Kyari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sa-labule a fadar shugaban kasa na Aso Villa da shugaban kamfanin NNPC na kasa.

A yau Laraba, 8 ga Watan Junairu ne mu ka samu labarin wannan muhimmiyar tattaunawa tsakanin shugaban na NNPC da Buhari.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ba ta iya kawo ainihin dalilin wannan haduwa a rahoton da ta fitar a tsakiyar makon nan ba.

An yi wannan zama ne tsakanin shugaban Najeriyar da shugaban kamfanin man kasar a daidai lokacin da farashin danyen mai ya tashi.

KU KARANTA: Trump ya yi magana bayan Iran ta kai hare-hare a sansanin Soji

Shugaban kasa Buhari ya shiga muhimmiyar ganawa da Mele Kyari
Kudin danyen mai ya tashi da 2.4% a kasuwar waje a makon nan
Asali: UGC

Gangar mai ya kara kudi a kasuwa ne a sakamakon rikicin da ya ke neman barkewa a Yankin Gabas ta tsakiya tsakanin Iran da Amurka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gangar man fetur ya dada kudi a Duniya bayan Sojojin Amurka sun hallaka wani babban Sojan kasar Iran.

NAN ta ce shugaba Muhammadu Buhari zai kuma yi wani irin wannan zama an jima da karamin Ministan fetur na Najeriya, Timipre Sylva.

Kudin danyen mai ya yi tashin ta Najeriya ta fara saida ganga guda a kan $70, karon farko da mai ya yi kudi haka tun Watan Yunin 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng