Garin dadi na nesa: Gwamnatin kasar Finland za ta kawo tsarin aikin kwana 4 a mako, sannan aikin awa 6 a kowacce rana

Garin dadi na nesa: Gwamnatin kasar Finland za ta kawo tsarin aikin kwana 4 a mako, sannan aikin awa 6 a kowacce rana

- Kasar Finland zata kirkiro da kwanakin aiki hudu kacal a mako

- Wannan gyaran zai samu shugabancin Sanna Marin ne

- Kamar yadda rahoto ya bayyana, gyaran zai ba ma’aikata damar samun lokacin iyalinsu da al’adu

Firaye minista mafi karancin shekarau, Sanna Marin, ta kasar Finland zata kirkiro kwanaki hudu na aiki da kuma sa’o’i shida na aiki.

Firaye ministan mai karancin shekaru zata bar ma’aikata su fara samun isasshen lokaci da iyalansu da abokai. Hakan kuwa zai taimaka musu wajen walwala da samun lokacin tabbatar da al’adu.

“Ya kamata mutane su samu isasshen lokaci da iayalai, abokai da ‘yan uwa. Hakan zai tabbatar da wanzuwar walwala da farin ciki. Wannan zai zamo abinda zamu fara aiki a kai,” cewar firayem minister Sanna Marin.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa a kasar Finland ma’aikata na aikin sa’o’i takwas a rana ne kuma da kwanaki biyar a mako.

KU KARANTA: Ni ba Musulmi ba ne, amma na san Annabi Muhammadu shine mutumin da yafi kowa a duniya - Chicharito

Legit.ng ta ruwaito yadda kasar Finland ta zabi shugaba mafi karancin shekaru a tarihi a ranar 8 ga watan Disamba 2019, wanda kuma ita ce ministan sufuri mai shekaru 34 a duniya ta kasar kafin zabenta.

Nasarar Marin ta biyo bayan yadda jama’ar kasar suka cire rai daga Antti Riinne ta yadda ya kasa shawo kan matsalar yajin aiki a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel