Na karanta Qur'ani sau 6, Islam addini ne na zaman lafiya - Babban Fasto, Apostle Suleiman

Na karanta Qur'ani sau 6, Islam addini ne na zaman lafiya - Babban Fasto, Apostle Suleiman

Na sauke Qur’ani sau shida kuma ban ga inda aka umarci musulmi da ya kashe rai ba. Addinin musulunci addini ne na salama da zaman lafiya, cewar Apostle Sulaiman.

Wanda ya kirkiro Omega Fire Ministry, Apostle Johnson Suleiman ya mayar da martani a kan kisan Kiristoci 11 da mayakan ISWAP suka yi a ranar Kirsimeti.

Kamar yadda Apostle Johnson Suleiman ya mayar da martanin a shafinsa na tuwita, ya wallafa cewa: “Qur’ani yace duk wanda ya kashe rai daya tamkar ya kashe dukkan jama’a ne… ISWAP shaidanu ne kuma Ubangiji zai hukunta su. Kun kashe Kiristaci 11 ko?

DUBA WANNAN: Badakalar daukan aiki: Matawalle ya dakatar da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara

A shekarun da suka shude, na sauke Qur’ani har sau shida… Babu musulmi nagari da zai iya kashe wani mutum… Musulunci addinin salama ne.”

Wadannan kalaman sun jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita.

Wasu daga cikin masu bibiyar shafin nashi sun zarge shi da fara da'awa zuwa addinin musulunci. Amma wasu sun tabbatar masa da bai karanta Qur’anin da kyau bane shiyasa bai ga inda aka umarci musulmi da su kashe kafirai ba don samun tikitin shiga aljanna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel