Yadda na rasa N25bn a Legas - Dangote

Yadda na rasa N25bn a Legas - Dangote

Attajirin dan kasuwan Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya ce cinkoson da ke hanyar tashan jirgin ruwa na Apapa ya janyo wa kamfaninsa asarar kudin shiga da ya kimanin Naira biliyan 25 a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019.

Aliko Dangote ya bayyana hakan ne a Legas a ranar Litinin yayin da ya zagawa da ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola don nuna masa titi mai tsawo kilomita 35 na Apapa-Oshodi-Oworonsoki-Ijota da halin yanzu Dangote Industries Limited (DIL) ke ginawa.

Ya shaidawa Mista Fashola cewa babban titin na Apapa-Oshodi zai yi shekaru 40 ana amfani da shi.

Da ya ke tsokaci a kan yanayin kyawun titin da ake ginawa, ya ce titin zai farfado da harkokin kasuwanci a unguwar ta Apapa.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Dangote ya ce, "Wannan titin zai fadada tattalin arziki. Zai samar da ayyuka masu yawa kuma masana'antu da dama da suka fice daga unguwa za su dawo.

"Muna fatan hakan ya faru a karshen shekarar 2020, a lokacin za a kammala dukkan aikin titin; Za a gina titin da zai yi shekara 40 ana morar sa."

A bangarensa, Fashola ya ce, "Gwamnatin tarayya za ta cigaba da bayar da goyon baya don ganin an kammala aikin titin domin kawo karshen matsalolin rashin tituna masu kyau da cinkoso."

Ya kara da cewa: "Kasuwanci ya fara habbaka a Liverpool road duk da cewa an rufe layin a baya amma yanzu an bude. Za ku cigaba da ganin hakan. Dukkan masana'antu da sauran kasuwanci da suke durkushe a Creek road za su dawo. Muna sa ran ganin gine-gine da sauran ayyuka da zarar an kammala titin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel