Ganduje Dattijo ne kuma gogaggen ‘Dan siyasa mai kishin kasa – Tinubu

Ganduje Dattijo ne kuma gogaggen ‘Dan siyasa mai kishin kasa – Tinubu

A wani sakon taya murna zuwa ga gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan ya cika shekara 70, Bola Tinubu, ya jinjinawa gwamnan Kano.

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, wanda ya na cikin Jagororin jam’iyyar APC mai mulki ya godewa Ubangiji da ya ba Ganduje irin wannan dama.

“Kai Dattijo ne, ‘Dan siyasa wanda aka dade ana gogawa da su. A matsayinka na Dattijo kuma Maras nuna banbancin kabila, ka na yi wa kowa kallon daya.”

Bola Tinubu ya cigaba da cewa: “Ka na cigaba da yin hidima domin hadin-kai da zama lafiyan kasar nan, kuma da kokarin dinke kan mabanbantan mutane.”

“Wannan shaida ne game da irin kallo dayan da ka ke yi wa kasar nan, kai Surukin kasar Yarbawa ne wanda ake ganin mutuncinsa.” Inji Bola Tinubu.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da za su taimakawa Tinubu kai ga ci a zaben 2023

Tsohon Sanatan na Legas ya bayyana Abdullahi Ganduje a matsayin ‘Dan siyasa mai lissafi da dabara, wanda kuma ya san shugabanci da aiki da jama’a.

Jawabin ya ce: “Ka bada gudumuwa wajen cigaban jiharka da Najeriya, haka ka sadaukar da kanka wajen habaka da cigaban jam’iyyar nan ta mu ta APC.”

“Babu mamaki ake kiranka wajen dinke baraka da sasanta rikicin jam’iyyarmu ta APC."

Addu’armu shi ne Allah ya cigaba da kara maka lafiya, da shekaru da kwarin gwiwa domin cigaba da yi wa jiharka da kasarmu bauta bakin gwargwado.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel