Tsaro: Jerin sunayen sabbin AIG da kwamishinonin da IGP ya nada

Tsaro: Jerin sunayen sabbin AIG da kwamishinonin da IGP ya nada

Sifeta Janar din 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin sauyin wajen aiki ga AIG Sanusi Nma Lemu zuwa yanki na 12, Bauchi (jihohin Bauchi, Borno da Yobe) da AIG Gwandu Abubakar zuwa yanki na 3, Yola (jihohin Adamawa, Gombe da Taraba).

Hakazalika an tura kwamishinonin 'yan sanda zuwa jihohi kamar haka: Kwamishina Hafiz Muhammed Inuwa zuwa jihar Delta, Kwamishina Muri Musa zuwa jihar Kaduna, Kwamishina Mobolaji Olaniyi Fafowara zuwa jihar Imo.

Sauran sun hada da Kwamishina Agunbiade O. Lasore zuwa jihar Kebbi, Kwamsihina Johnson Babatunde Kokumo zuwa jihar Osun, Kwamishina Ahmed Mohammed Azare zuwa jihar Taraba da Kwamishina Ede Ayuba Ekpeji zuwa jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Ganduje da Sanusi: Ganduje ya kauce wa kwamitin sulhu, ya tafi Umrah

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Frank Mba, ya yi bayanin cewa IGP ya yi kira ga jami'an da abun ya shafa da su dasa a kan nasarar da wadanda suka gada suka kafa.

Ya kara kira dasu da su dage wajen hada kai da masu ruwa da tsaki don samun bayanai masu amfani da zasu taimaka musu wajen yakar laifuka.

Ya kara da kira ga jama'a da su goya wa sabbin jami'an tsaron baya don sauke nauyinsu na kare rayuka da dukiyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel