Abin da ya sa N37bn ba zai isa a gyara Majalisar Tarayya ba – Inji Agada

Abin da ya sa N37bn ba zai isa a gyara Majalisar Tarayya ba – Inji Agada

Jama’a sun hurowa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wuta a game da shirin da ta ke yi na batar da biliyoyon kudi da sunan gyaran majalisar tarayya.

Duk da wannan surutu da jama’a su ke yi, wani jami’in da ke kula da majalisar kasar, ya fito ya nuna cewa ba dole bane ma kudin da za a kashe su wani isa.

Darektan yada labaran majalisar, Rawlings Agada, ya ce wannan kudi Naira biliyan 37 za su iya yin kadan a wajen aikin saboda gyaren gaske ginin ya ke bukata.

A makon da ya gabata ne ‘Yan majalisar su ka amice da wannan kudi da nufin za su yi wa harabarsu da cikin ginin majalisar wasu ‘yan kwaskwarima.

KU KARANTA:

Shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya shaidawa ‘Yan jarida cewa shugaban kasa ya san da wannan magana, kuma har an sa kudin wannan aiki a kasafin kudi.

Rawlings Agada ya ce ginin yadda majalisar ya sukurkuce kuma har ta kai kubban ginin ya dade ya na yoyo, a cewarsa, wannan gyara zai bukaci kudi sosai.

Agada ya cewa Manema labarai: “Majalisar tarayya na bukatar gyara sosai, kuma ina tunanin ko wannan kudin ba za su isa ayi duk aikin da ake bukata ba”

“Har kubban ginin yoyo ya ke yi, kuma ana tsoron idan ba ayi wannan gyara ba, nan gaba matsalar da za a gamu da ita za ta yi kamari.” inji Agada.

Darektan ya kara da tabbatar da cewa: “Ban san takamaimen aikin da za ayi ba, saboda ba ni da kundin kasafin kudin, amma dai na san cewa aiki za ayi sosai.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng