Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo

Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo

Fitaccen dan wasan kungiyar Real Madrid mai rike da kambun zakarar dan kwallon kafa na Duniya gaba daya, Cristiano Ronaldo ya yi barazanar raba gari da kungiyarsa matukar suka siyo dan wasan Liverpool Mohammed Salah.

Daily Trust ta ruwaito labarai dake yaduwa a kasar Sifaniya sun bayyana cewar Ronaldo baya kaunar kungiyarsa ta siyo duk wan dan wasa da zai dusashe tauraruwarsa.

KU KARANTA: Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu

Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo

Jaridar Don Balon ta bayyana cewar tuni Ronaldo ya tabbatar ma kungiyarsa cewar da zarar sun siyo Salah, to fa angulu za ta koma gidanta na tsamiya, watau zai iya komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Bugu da kari, rahotannin sun kara da cewa Ronaldo na kwadayin kungiyarsa ta bashi girmansa, kamar yadda Barcelona da PSG ke girmama Messi da Neymar, musamman duba da cewa ya kaisu ga wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai har sau hudu.

Zuwan Salah Madrid: Ba ai mani kishiya – Inji Cristiano Ronaldo
Salah

Haka zalika rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa ita ma kungiyar Manchester ta shirya tsaf ta karbi tsohon dan wasan na ta, musamman a yanzu da kocin kungiyar, Jose Mourinho ke tsananin bukatar muhimman dan wasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel