Abubuwan da kundin kasafin kudin Najeriya na shekara mai zuwa ya kunsa

Abubuwan da kundin kasafin kudin Najeriya na shekara mai zuwa ya kunsa

A Ranar Talata, 17 ga Watan Disamban 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan sabon kasafin kudin da Najeriya za ta yi amfani da shi a shekarar 2020 mai zuwa.

Mun kawo canjin da aka samu tsakanin kasafin kudin da shugaban kasar ya gabatarwa majalisa a watannin baya, da kuma kundin kasafin da ya sa wa hannu bayan an yi wasu kwaskwarima.

1. Adadin kudin da za a kashe

Shugaba Buhari ya sa ran kashe Naira tiriliyan 10.33 ne a shekarar badi. Amma majalisar tarayya sun kara buri, inda su ka yi sama da kudin da za a batar da biliyan 260 zuwa Naira tiriliyan 10.56.

2. An kara yawan kudin albashi

Majalisar tarayya ta kuma kara yawan abin da gwamnatin Najeriya za ta batar a kan albashi a 2020. Buhari ya yi lissafin Naira tiriliyan 4.84, sai majalisa ta kara miliyan 400 zuwa tiriliyan 4.84.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2020

3. Ayyukan more rayuwa

Kamfanin BudgIT mai bin diddikin yadda ake kashe kudi a Najeriya ta bayyana cewa kudin da aka ware domin ayyukan more rayuwa sun tashi daga tiriliyan 2.45 zuwa tiriliyan 2.72 a 2020.

4. Kudi wasu hukumomi

Kudin da ake warewa wasu ma'aikatu masu cin gashin kansu kamar majalisa, bangaren shari’a, da irinsu INEC, ya karu. Abin da za su kashe yanzu ya tashi daga miliyan 556 zuwa miliyan 560.

5. Biyan bashi

Haka zalika majalisar tarayya ta yi kwaskwarima game da batun kudin bashi. Abin da Najeriya ta ware domin biyan bashi a kasafin kudin badi ya koma Naira tiriliyan 2.72 daga tiriliyan 2.45.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel