Gwamna Makinde ya bawa dan Kano mukami a gwamnatinsa

Gwamna Makinde ya bawa dan Kano mukami a gwamnatinsa

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo na nada Alhaji Ahmed Murtala, dan asalin jihar Kano a matsayin mai taimaka masa na musamman a kan harkokin unguwanni na I.

Ya kuma nada Mista Femi Josiah a matsayin mai taimaka masa na musamman a kan harkokin unguwanni na II kamar yadda NPO reports ta ruwaito.

Makinde ya kuma amince da nadin Dakta Olufunmilayo Salami a matsayin mai bayar da shawara ta musamman a kan Lafiya yayin da ya nada Cif Jacob Adetoro a matsayin shugaban ofishin sadarwa na mazabun tarayya.

Sanarwar ta gidan gwamnati ta fitar ta ce gwamnan ya nada jami'an sadarwa na mazabu 14 da ke wakiltan kowanne mazaba a jihar a tarayya.

DUBA WANNAN: Mijina ne ya bani shawarar na ke zina da maza daban-daban - Matar aure ta fada a kotu

A cewar sanarwar, Murtala dan asalin karamar hukumar Nasarawa ce a jihar Kano kuma ya yi makarantar frimare a St. Brigid Boys School, Makola, Ibadan kana ya yi sakandare a Community Grammar School da ke Makola, Ibadan.

Sanarwar ta ce; "Murtala zai zama wakili kuma mai sada zumunci tsakanin gwamnatin jihar Oyo da al'ummar hausawa da fulani da ke garin da sauran 'yan arewa a jihar.

"Dakta Salami kwararriya ce a fanin lafiya a jihar kafin nadin ta a matsayin mai bayar da shawara na musamman.

"Likitan yara ne na gaggawa a kasar Amurka kafin ta dawo Najeriya.

"Gwamna Makinde ya umurci wadanda aka yi wa nadin su dauki shi a matsayin dama ta yi wa kasar su hidima kana suyi aikinsu cikin gaskiya da amana da nagarta. Ya ce nadin su zai fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Nuwamba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel