Tirkashi: Wata mata ta kashe danta na cikinta saboda ya koma dan luwadi

Tirkashi: Wata mata ta kashe danta na cikinta saboda ya koma dan luwadi

- Wani alkali a kasar Brazil ya yankewa wata mahaifiya shekaru 25 a gidan maza a kan laifin kisan danta

- Ta hallakashi har lahira ne da taimakon wasu 'yan daba biyu, saboda matashin dan luwadi ne

- Bayani daga kawun matashin ya nuna cewa, Lozano yaro ne na gari kuma mai saukin kai kafin mutuwarshi

An yankewa wata mata hukuncin shekaru 25 a gidan yari a kasar Brazil, bayan da aka kamata da laifin kashe danta saboda yana luwadi.

Matar da aka bayyana sunanta da Tatiana Ferreira Lozano Pereira, an yanke mata hukuncin zaman gidan maza ne na shekaru 25 da watanni 8, a kan laifin kisan Itaberli Lozano mai shekaru 17 a duniya. Ta aikata kisan da kanta ne bayan da ta tura a bukaci taimakon kasheshi a watan Disamba 2016 amma ba a samu nasara ba.

Dan sanda mai kara yace, Pereira ta yi hayar 'yan daba biyu don kashe matashin. Sun yi mishi dukan tsiya bayan da mahaifiyar ta yaudareshi ya je gida, da zummar zasu tattauna kuma su sasanta.

Bayan da 'yan dabar ba su yi nasara ba, ta sokeshi da wuka inda ya mutu har lahira, mujallar Out ta ruwaito.

KU KARANTA: Za a bawa Kwamaret Muhammad Ali kason shi na kasafin kudin Najeriya, bayan ya nemi a bashi hakkinshi a wani sabon bidiyo

Pereira ta amsa laifin kisan danta da hannunta yayin zaman kotun, saboda ya kasance barazana a rayuwarta.

Kawun Lozano na bangaren mahaifi, ya tabbatar da cewa yaron na da tarbiya, amma mahaifiyar ta tsaneshi ne saboda luwadin da yake yi.

"Yana da aikin yi kuma akwai kyan hali. Baya taba fada da kowa. Matsalar mahaifiyarshi itace, luwadin da yake yi." Cewar kawun Lozano.

Alkalin ya yankewa mahaifiyar hukuncin shekaru 25 da watanni 8 a gidan maza. Sai 'yan dabar da ta gayyata zasu yi shekaru 21 da watanni 8 a gidan yari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel