Zai gane kurensa: Dakarun Sojojin Najeriya cafke da wani sojan bogi

Zai gane kurensa: Dakarun Sojojin Najeriya cafke da wani sojan bogi

Rundunar sojojin Najeriya ta 82 Division a Enugu a ranar Alhamis ta ce ta kama wani sojan bogi kuma ta gano kungiyar wasu miyagu da ke satar wayoyin wutar lantarki a Nsukka cikin sabon atisayen da suke mai suna 'Exercise Atilogwu Udo 1."

Daily Trust ta ruwaito cewa babban kwamandan 82 Division na rundunar sojin Najeriya a Enugu, Manji Janar Lasisi Adegboye ya ce dakarun sector 5 na Enugu ne suka kama miyagun yayin da ya ke zantawa da manema labarai.

Acewar Adegboye, tun bayan fara atisayen an samu nasarar dakile barazana masu yawa a sassa daban-daban na jihar tare da taimakon wasu hukumomin tsaro a 82 Division.

Kwamandan ya ce: "A ranar Talata 26 ga watan Nuwamba, Dakarun Sector 5 na atisayen Atilogwu Udo 1 yayin sintiri sun kama wani Mista Madukwe Obinna a Nsukka, Enugu yana gabatar da kansa a matsayin soja.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

"Wanda ake zargin yana cikin wata mota ne da ke dauke da yalo daga Abuja zuwa jihar Abia; binciken da aka fara gudanarwa sun nuna direban ya rage masa hanya ne saboda ya yi ikirarin cewa shi soja ne.

"Abubuwan da aka samu a tare da shi sun hada da naira 1000 ta bogi, Yen na kasar Japan, bindigar wasan yara, katin shaidan dan sanda na bogi, takardu masu dauke da tamburan sojojin Najeriya, takalmin sojoji, hulunnan injiniyoyi 2, alon suna mai dauke da sunan Madukwe O.I. da wuka."

Ya ce za a mika wanda ake zargin hannun 'yan sanda da jami'an NSCDC a jihar Enugu domin su zurfafa bincike.

Kwamandan ya bawa al'ummar jihar tabbacin cewa za su cigaba da jajircewa wurin aikinsu na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma tare da neman hadin kan al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel