EFCC: An yankewa Lauya hukuncin dauri a kan neman rashawar N7m a Borno

EFCC: An yankewa Lauya hukuncin dauri a kan neman rashawar N7m a Borno

Mun samu labari cewa Alkali ya yankewa Lauyan da ya bukaci a ba shi cin hanci na miliyoyin kudi. Kotu ta nemi a daure shi a gidan yari na watanni 18 ba tare da ba shi damar biyan tara ba.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa a Najeriya, ta bayyana cewa Alkalin babban kotun jihar Borno, ya yankewa Zanna Dalhatu daurin shekara daya da rabi.

Kamar yadda EFCC ta rahoto da kanta a jiya, Alkali mai shari’a Umaru Fadawu na babban kotun Borno, ya samu wannan Lauya na gwamnati da laifin neman cin hanci na Naira miliyan 7.

An gurfanar da Dalhatu, mai aiki da ma’aikatar shari’a ta jihar Borno, a gaban kotu ne a farkon Watan Junairun 2019 bayan hukumar EFCC ta damke shi bisa zargin neman karbar rashawa.

Dalhatu ya bayyanawa kotu cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba. Amma a karshen shari’a, Alkali Umaru Fadawu ya tabbatar da rashin gaskiyar jami’in shari’ar a Ranar Litinin.

KU KARANTA: Ka da a bude iyakokin kasa don Allah - Sanata ya roki Buhari

Kakakin hukumar EFCC na kasa, Wilson Uwujaren, ya sanar da jama’a cewa, Dalhatu ya nemi karbar rashawa daga hannun wani Akawu da ke aiki a ma’aikatar gyaran hanyoyi na jihar Borno.

Jami’in shari’ar ya nemi wannan babban Akawu mai suna Shuaibu Mohammed, ya biya cin hanci domin a dakatar da shari’arsa da ake yi da wani Ma’aikacin hukumar gyaran hanyoyin jihar.

Labarin ya shiga kunnen EFCC inda aka cafke shi ya na kokarin karbar wannan cin hanci. A bisa haka ne aka maka shi a gaban kotu har kuma aka gabatar da shaidu uku domin a hukuntasa.

Lauyan ya yi kokarin yi wa shari’a gardama, ya na mai daukaka kara a gaban wani babban kotu da ke Jos, amma bai dace ba. Daga baya ya amsa laifinsa, kuma aka yanke masa dauri a kurkuku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel