Fasa daukan 'yan sanda 10,00 asara ce ga tattalin arziki - Ministan Buhari

Fasa daukan 'yan sanda 10,00 asara ce ga tattalin arziki - Ministan Buhari

Abubakar Malami, ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), ya ce soke daukan sabbin 'yan sanda 10,000 da rundunar 'yan sanda ta yi zai zama asara ga tattalin arzikin kasa.

Malami ya bayyana hakan ne a cikin takardar kalubalantar hukuncin soke daukan sabbin kananan 'yan sandan 10,000 da wata kotu ta yi sakamakon karar da hukumar kula da harkokin 'yan sanda (PSC) ta shigar.

An samu sabani da rabuwar kai a tsakanin rudnunar 'yan sanda (NPF) da hukmar PSC a kan batun daukan sabbin kananan 'yan sanda 10,000.

PSC ta garzaya da kotu da bukatar neman ta soke daukan aikin da rundunar 'yan sanda ta yi, saboda doka ita ta dora wa alhakin daukan ma'aikatan rundunar 'yan sanda.

Sai dai, Malami, wanda sunansa na daga cikin wadanda aka shigar da kara, ya nemi kotun ta yi watsi da karar da PSC ta shigar.

Malami ya bayyana cewar alhakin NPF ne ta dauki sabbin ma'aikata, yayin da ita kuma hukumar PSC alhakinta ne yin karin girma ga jami'an 'yan sanda da ke cikin aiki.

DUBA WANNAN: IGP ya daure mahaifina saboda aurena da abokinsa ya mutu - Wata mata ta koka

"An bi dukkan ka'idojin da suka dace domin tantance mutanen da suka dace a dauka aikin," a cewar Malami a cikin takardarsa ta kalubalantar hukuncin kotun.

Sannan ya cigaba da cewa, "an kashe miliyoyi wajen daukar sabbin 'yan sandan, fasa daukan aikin zai zama asara ga tattalin arziki. Alhakin rundunar 'yan sanda da IG ne su dauki sabbin ma'aikata."

A cikin watan Satumba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da IGP, Mohammed Adamu, da Musliu Smith, shugaban hukumar PSC, domin sulhunta sabanin da ke tsakaninsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel