Kallo ya koma sama: Suruki ya sa Yansanda sun kama ASD, dansa da kuma Alkalin a Kaduna

Kallo ya koma sama: Suruki ya sa Yansanda sun kama ASD, dansa da kuma Alkalin a Kaduna

Jami’an Yansanda dake yaki da yan fashi da makami na rundunar Yansandan Najeriya sun kama tsohon shugaban kamfanin Pijo Najeriya, kuma fitaccen attajiri a garin Kaduna, Alhaji Sani Dauda a kan rikici daya biyo aurar da diyarsa da ya yi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito surukin ASD, kuma tsohon mijin diyarsa Naseeba ne ya umarci Yansanda su kama Alhaji Sani Dauda, tare da dansa Shehu Dauda da kuma alkalin kotun Musulunci dake Magajin gari, Murtala Nasir, wanda shi ne ya daura auren Naseeba da wani sabon miji.

KU KARANTA: Yanzun nan: Gobara ta tashi a fadar gwamnatin jahar Neja dake Minna

Majiyarmu ta ruwaito an daura auren Naseeba da wani mijin ne a ranar Asabar, 9 ga watan Nuwamba, wanda hakan ya matukar bata ma tsohon mijinta rai, da wannan yasa Yansanda suka kama masa mahaifinta da sauran mutanen biyu a ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba.

A yanzu haka ana rike mutanen uku a babban ofishin Yansandan SARS dake garin Kaduna, kamar yadda lauyan wadanda aka kama, Sani Katu ya bayyana ma manema labaru, inda ya tabbatar da cewa tsohon mijin Naseeba ne ya kamasu.

Sai dai koda majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Yakubu Sabo domin jin ta bakinsa, sai yace ba shi da masaniya game da bahallatsar, amma zai yi karin bayani da zarar ya tabbatar.

A wani labarin kuma, hankula sun tashi a unguwar Mahutan jahar Kaduna dake cikin karamar hukumar Igabi ta jahar, inda wasu gungun miyagun yan bindiga suka yi awon gaba da wani malamin jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria, Adamu Chinoko.

Jama’a sun kara shiga halin kidimewa ne yayin da dan uwansa mai suna Umar Chinoko, wanda shi ma malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna ya tafi ya kai musu kudin fansa kamar yadda suka bukata, amma suka sake yin garkuwa da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel