Maulidi: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Litinin a matsayin ranar hutu

Maulidi: Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Litinin a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Litinin, 11 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan Najeriya domin gudanar da murnar tunawa da ranar haihuwar manzon Allah, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito daraktan watsa labaru na ma’aikatan cikin gida, Mohammed Manga ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Aikin jin kai: Aisha Buhari ta tallafa ma mata da matasa 600 a jahar Adamawa

Manga yace, Ministan cikin gida, Abdulrauf Aregbesola na taya Musulmai murnar zagayowar wannan rana, sa’annan yana kira ga Musulmai da su yi rayuwa daidai da koyarwar manzon Allah.

Ministan ya kara da cewa: “Koyi da kyawawan halayen Annabi kamar soyayyar juna, kwazo, da juriya ne kadai zai tabbatar da zaman lafiya da samar da tsaro a Najeriya.”

Haka zalika, Minista Aregbesola ya bayyana tabbacinsa na samun sauki game da kalubalen da Najeriya ke fuskanta, inda yace nan gaba kadan za’a nemisu a rasa, don haka ya yi kira ga yan Najeriya dasu kasance masu kokari da kwazo.

Bugu da kari Aregbesola ya bada tabbacin duba da tarin arzikin kasa da Allah Ya yi ma Najeriya, tare da yawan jama’anta, nan bada jimawa Najeriya za ta shiga sahun sa’o’inta da suka samu gagarumar cigaba.

“Da soyayyar juna, jajircewa, sadaukarwa, hakuri da kuma kishin kasa zamu gina Najeriya ta zama kasa mai kima a idon duniya.” Inji Ministan.

A wani labarin kuma, uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta bayar da tallafi ga mata da matasa 600 a jahar Adamawa a karkashin ayyukan gidauniyarta ta Future Assured Foundation, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyarmu ta ruwaito babban jami’in dake kula da ayyukan gidauniyar Future Assured, Alhaji Yau Babayi ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba a birnin Yola, inda yace gidauniyar ta tsamo mutane 600 daga kananan hukumomin jahar 21 daga kangin talauci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel