El-Rufai, Sarakuna, hafsoshin tsaro da yan majalisu sun goga gemu da gemu a kan tsaron Kaduna

El-Rufai, Sarakuna, hafsoshin tsaro da yan majalisu sun goga gemu da gemu a kan tsaron Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi wata ganawar sirri tare da dukkanin masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro a jahar Kaduna, inda suka goga gemu da gemu tare da musayar ra’ayi a kan yadda za’a shawo kan matsalar tsaro a Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace wannan ganawa ta gudana ne a ranar Laraba, 6 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin jahar Kaduna, Sir Kashim Ibrahim House.

KU KARANTA: El-Rufai ya kara nada sabbin hadimai guda 18 a fadar gwamnatin Kaduna

Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya gana da shuwagabannin siyasa da masu rike da sarautun gargajiya na kananan hukumomin Igabi, Chkun da Birnin Gwari tare da shuwagabannin hukumomin tsaro, inda ya yi musu cikakken bayani game da kokarin da yake yi wajen shawo kan matsalar tsaro a kananan hukumomin 3 da ma jahar gaba daya.

Haka zalika suma shuwagabannin tsaron sun bada bahasin aikace aikacen da suke yi wajen tabbatar da tsaron dukiya da rayukan al’ummomin kananan hukumomin uku. Daga nan kuma sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki sun bayar da shawarwarin da suke ganin zasu haifar da da mai ido.

Daga karshe shuwagabannin tsaron sun bayyana wasu sabbin matakai da zasu fara dauka wajen shawo kan matsalar tsaro a kananan hukumomin, wanda gaba daya mahalarta zaman suka amince dasu.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai yan majalisa wakilai 3 Yakubu Umar Barde-Chikun/Kajuru, Shehu Balarabe- Birnin Gwari/Giwa da Zayyad Ibrahim-Igabi. Sai yan majalisun jaha 8; Yusuf Ibrahim Zailani-Igabi ta yamma, Haruna Inuwa-Doka/Gabasawa, Abdulwahab Kurminkogi-Ikara, Ayuba Chawaza-Chikun, Salisu Isah-Magajin Gari, Bala Umar-Kakangi, Shehu Yunusa-Kubau da Suleiman Ibrahim Dabo-Zaria City.

Haka zalika akwai Sarakuna kamar su Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Jibril Zubairu II da Sarkin Chikun, Dr Danjuma Barde. Da kuma kwamishinan sharia Aisha Dikko, kwamishinan kananan hukumomi Jafaru Ibrahim Sani, kwamishinan kare fadace fadace Hassan Usman da kwamishinan tsaro Samuel Aruwan.

Daga bangaren jami’an tsaro kuwa akwai kwamandan Soja Birdediya janar OJ Akpor, kwamandan kwalejin kimiyya da fasaha ta Sojan ruwa Commodore Yakubu Pani, kwamandan sansanin sojan sama Air Commodore Ibrahim Sani, shugaban DSS na Kaduna Idris Koya da BA Dutsinma kwamandan NSCDC, da kuma Kanal Francis Omata dake wakiltar Operation Safe Haven.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel