Rainin wayo: Mai laifi ya zama mahaukacin karya, ya tsula fitsari cikin kotu

Rainin wayo: Mai laifi ya zama mahaukacin karya, ya tsula fitsari cikin kotu

An garkame wani mai laifi, Ibrahim Saheed, a gidan yarin Ilesha, jihar Osun, bayan zama mahaukacin karya a cikin kotu.

An gurfanar da Saheed gaban kotun majistaren Alkali Opeyemi Badmus dake birnin Osogbo kan zargin aikata fashi da makami.

Yace: "Ba ni bane, karya suke min. Bani nayi kokarin yi masa fashi ba. Ya kasance makwabcina a Abere na tsawon lokaci."

Alkalin ya tambayi wanda ya shigar da kara, AbdulSalam Raji, shin ya san Saheed. Raji ya ce bai san shi ba kuma basu taba zama gida daya ba.

Yace karon farko da ya taba ganinsa shine lokacinda suka kawo masa hari misalin karfe 2:15 na daren ranar Juma'a, 25 ga Oktoba, 2019.

Sai Saheed ya bukaci Alkalin ya bashi daman fita wajen fitsari, kafin Alkali ya bashi amsa, kawai sai ya fara tsula fitsari a cikin kotu.

Lauyan yan sanda, Elisha Olusegun, ya ce Saheed ya raina musu wayo ne kawai amma lafiyarsa kalai kafin shiga kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel