Garar N30: Nanono yaki amsawa manema labari tambayarsu

Garar N30: Nanono yaki amsawa manema labari tambayarsu

- Ministan aiyukan noma, Alhaji Sabo Nanono, ya kaucewa tambayar manema labarai akan garar naira talatin kacal

- Ya yi hakan ne a taron da yayi da manoma tare da masu ruwa da tsaki a cikin birnin Kano

- Ministan ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf don farfado da masaku na kasar nan

Ministan aiyukan noma, Alhaji Sabo Nanono, a jiya ya kaucewa tambayar manema labararai akan ikirarin samun abicin naira talatin da yayi.

Nanono, da yayi taro da manoma da masu ruwa da tsaki a kano, ya jaddada cewa ba zai yi tsokaci akan lamarin mai rudani ba.

KU KARANTA: Safiyya Ahmad, ta lashe gasar Hikayata na bana

Ministan ya sha buhu-buhun kalubale sakamakon cewa da yayi abinci na arha kuma ana iya samun abinci mai rai da motsi a naira talatin kacal a Kano bayan habakar da aka samu a bangaren abincin kasar nan.

A taron, ministan ya sanar da tsare-tsaren gwamnatin tarayyar na farfado da masakun da ke jihar Kano.

Ministan da ya bayyana tsananin alhininsa sakamakon zaman Najeriya kan gaba wajen shigo da kayan sawa, ya ce za a farfado da masakun ne don kara habaka tattalin arzikin kasar nan.

Nanono ya tabbatar da gwamnatin Buhari ta maida hankali wajen ganin ta kawo cigaba ta bangaren noma ta hanyar jawo hankulan masu saka hannayen jari a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel