Ba laifi bane ka yi 'amai ka lashe' - Sule Lamido ya fada wa su Kwankwaso

Ba laifi bane ka yi 'amai ka lashe' - Sule Lamido ya fada wa su Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba laifi bane kuma ba abin kunya bane ga wadanda suka bar jam'iyyar PDP su sake dawowa cikinta.

Lamido ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taron jam'iyyar PDP da aka yi domin maye gurbin shugabannin jam'iyyar PDP da suka sauya sheka a jihar Jigawa.

"Ba abun kunya bane mutum ya yi amai ya lashe a siyasa, babu dole a batun akidar siyasa," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Kwastam sun gano wani gida da ake canjawa shinkafa buhu, sun kama mutum 15 (Hoto)

Da yake magana a kan wadanda suka canja sheka saboda PDP ta fadi zabe, Lamido ya ce, "Wadanda suka bar jam'iyyar PDP saboda mun zabe, nan bada dadewa ba zasu gane cewa PDP ce jam'iyyar da aka gina bisa akidun son cigaban jama'a da yin tafiya da mutanen da suka cancanta."

Dangane da wasu manyan 'yan siyasa, irin su Kwankwaso, da suka bar PDP kuma suka dawo, Lamido ya ce, "zabin yaro ne ya cigaba da kwanciya a kan gadon mahaifiyarsa bayan ya yi fitsarin kwance ko kuma ya canja wurin kwanciya idan ba zai iya hakuri kazantar da ya yi ta bushe ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel