Jami’ar Adamawa ta bayyana wata matsalar da ke ci mata tuwo kwarya

Jami’ar Adamawa ta bayyana wata matsalar da ke ci mata tuwo kwarya

Daliban Jami’ar Jihar Adamawa wato ADSU sun yi kira na a duba al’amuran jami’ar da suka shafi kudade da kuma karin lakcarori domin magance matsalolin jami’ar.

Wakilai Kuniyar daliban jami’ar ne suke mika wannan koken ga sabbin ‘yan majalisar gudanarwar jami’ar. Kungiyar ta SUG ta fadi wannan sakon ne a lokacin da take ganawa da majalisar gudanarwar.

KU KARANTA:Wani mutum mai shekaru 63 kashe matarsa har lahira

Sakataren kungiyar daliban, Tizhe Geoffrey ya ce: “Ganawar mu da su tayi armashi sosai saboda mun fada masu abubuwa da dama da jami’armu ke bukata. Mun yi magana a kan karin kudin da ake bai wa jami’ar domin yin aikace-aikace.

“Muna da yakinin cewa, Gwamna Ahmadu Fintiri zai duba wannan bukatar tamu kasancewar yana da niyyar dawowa da martabar ilimi a jihar. Mun kuma yi magana game da karin malamai ta hanyar daukan dalibai mafi hazaka dake kammala karatu a sassa daban-daban na jami’ar.” Inji Sakataren.

Har ila yau, reshen Kungiyar malaman jami’a ta Najeriya wato ASUU, ta Jami’ar Adamawa tayi magana game da sabbin mambobin majalisar gudanarwar jami’ar. Inda ta ce kasancewar Jami’ar ta dade akwai abubuwa da dama da majalisar za ta fuskanta.

Abubakar Aliyu, wanda shi ne shugaban ASUU reshen Jami’ar Adamawa ya bukaci majalisar gudanarwar ta mayar da hankali a fannin tsaro na jami’ar. A cewarsa Mubi na daya daga cikin wuraren da ke fama da rikicin Boko Haram.

Rahotanni daga kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN sun bayyana mana cewa, Alhaji Auwal Tukur shi ne shugaba majalisar gudanarwar.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/adamawa-varsity-students-call-for-more-funding-recruitment-of-lecturers/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel