Rashin sa ido da iyaye ke yi ya sa tarbiyya ta lalace a jihar Kano - Sheikh Umar Fagge

Rashin sa ido da iyaye ke yi ya sa tarbiyya ta lalace a jihar Kano - Sheikh Umar Fagge

Wani shahararen malamin addinin Islama mazauni a jihar Kano, Sheikh Umar Sani Fagge, ya zargi rashin sa ido da kuma nuna halin ko in kula da iyaye ke yi a matsayin babban dalilin da ya haddasa lalacewar tarbiyya a jihar.

Sheikh Umar Fagge ya bayyana hakan ne a yayin wani muhimmin taro da aka gudanar a birnin Kanon Dabo, dangane da yadda za'a magance matsalolin ta'ammali da miyagun kwayoyi, fadan daba da sara-suka, karuwanci da sauran miyagun ababe na abun ki.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, an gudanar da taron ne kan maudu'in "lalacewar tarbiyyar al'umma da kuma hanyoyin kawo mafita" a ranar Juma'ar da ta gabata.

A yayin gargadin iyaye da su tsaya tsayin-daka wajen sa ido a kan 'ya'yan su, Sheikh Sani Fagge, ya bayyana damuwa a kan lalacewar tarbiyyar matasa ta yadda a koda yaushe ake tsintar su a cikin dukkanin wasu ababe na sharri.

Ya ce akwai bukatar hadin gwiwa a tsakanin al'umma, gwamnati da kuma iyaye domin shawo kan matsalar lalacewar tarbiyya a jihar Kano.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Zamfara ta gano sarakuna da jami'an tsaro masu hannu a matsalar tsaron jihar

A wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, 'yan matan Adamawa, sun nemi matar gwamnan jihar, Hajiya Lami Fintiri, ta shige masu gaba wajen tabbatar da an shimfida sabuwar doka da za ta haramta wa iyayensu aurar da su a kananun shekaru gabanin su kai munzali.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel