Bidiyo: Allah ya tona asirin wasu mazinata, yayin da mazakutar namijin ta makale jikin macen bayan sun gama lalatar su

Bidiyo: Allah ya tona asirin wasu mazinata, yayin da mazakutar namijin ta makale jikin macen bayan sun gama lalatar su

- Asirin wasu mazinata ya tonu yayin da suka makale a jikin juna bayan sun kammala lalata a wani otel

- Bayan sunyi sunyi su rabu sun kasa sai suka fara ihun neman taimako, inda mutane suka dauke su zuwa wajen wata bokanya domin ta raba su

- Wannan lamari dai ya faru a wani otel ne dake tsakiyar kasuwa, inda mutane suka yi dafifi domin kallon ikon Allah

Wani mutumi ya makale tsakanin kafafuwan wata mata bayan sun gama aikata lalatar su a wani dakin otel dake kusa da wata kasuwa a kasar Kenya.

Jaridar Nairobi News ta ruwaito mutanen sun fara ihun neman taimako ne bayan namijin yayi yayi ya kasa cire mazakutar shi daga jikin macen.

An dauki mutanen an kai su wajen wata mata mai maganin gargajiya, bayan mutane sunyi iya yin su sun kasa raba su.

Wanda lamarin ya faru a kan idon su sun ce, matar mai suna Sabina Moraa, dama can ana zargin ta wannan halayya ta bin maza duk kuwa da cewa tana da aure, hakan ya sanya mijinta yaje neman magani a wajen boka domin ya ganewa kanshi da idon shi. Bokan ya bashi wani magani da zan sanya mata.

KU KARANTA: Innalillahi: An ceto yaran Hausawa Musulmai 'yan Kano guda 9 da aka sace aka kai su Kudu aka canja musu suna aka mayar da su Kiristoci

A yayin da wasu suke ihun a bude suga mazinatan wasu kuma suna cewa a kira mijin matar ya zo ya taimaka ya karya maganin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar 'yan sanda na yankin, Philip Kimanzi, ya ce mutanen biyu sun makale a yayin da suke lalata a wani otel ita kuma matar da aka kaiwa ta karya asirin ta nemi wasu makudan kudade masu yawa.

Da aka tambayi bokar akan dalilin da ya sanya take bayar da irin wannan magani wanda zai tona asirin mutane, bokar mai suna Annete Mutheu ta bayyana cewa ta fito ne domin ta kawo karshen mutane irin wadannan a kasar Kenya.

Ga bidiyon yadda lamarin ya kasance a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel