Gwamnatin jahar Zamfara ta fara hada magunguna domin amfanin talakawa

Gwamnatin jahar Zamfara ta fara hada magunguna domin amfanin talakawa

Gwamnatin jahar Zamfara ta fara hada magunguna da kanta wanda za ta dinga rarrabawa ma asibitocinta domin al’ummar jahar su dinga samunsa cikin sauki da arha, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Gwamnan jahar, Bello Matawalle ya tabbatar da haka a ranar Laraba a garin Gusau yayin da yake gabatar da wasu magunguna guda 4 da hukumar kula da magunguna ta jahar Zamfara da hada.

KU KARANTA: Hari a matatar man kasar Saudi: Ba mu da hannu a ciki – kasar Iran

Majiyar Legit.ng ta ruwaito nan bada jimawa hukumar za ta shiga hada magungunan ganga ganga babu kama hannun yaro, kamar yadda Gwamna Matawalle ya tabbatar inda yace: “Mun sayo duk na’urori da injinnan da ake bukata wajen hada magunguna.

“Kuma zamu tabbatar da magungunanmu sun yi daidai da wanda manyan kamfanoni suke sarrafawa, fatanmu shi ne jama’an Zamfara da ma Najeriya gaba daya su samu ingantaccen magani daga wajenmu, zamu dinga kai ma duk cibiyoyin kiwon lafiya dake wannan jahar magunguna don kulawa da mutanenmu, zamu cigaba da kulawa da mata da kananan yara yan kasa da shekara 5 kyauta.” Inji shi.

Da yake nasa jawabin, shugaban hukumar, Aliyu Maikiwo ya bayyana cewa hukumarsu ta kai wasu daga cikin magungunan da ta hada zuwa jahohin dake makwabtaka da Zamfara, kuma sun yaba.

Sa’annan ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da suka hada kamarsu ruwan spirit, ruwan wanke hannu, ruwan sabulu da kuma turaren kanshi na daki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel