Yanzu-yanzu: Wani bene mai hawa uku ya ruguza a Onitsha

Yanzu-yanzu: Wani bene mai hawa uku ya ruguza a Onitsha

Wani ginin bene mai hawa uku da ke lamba 22 a titin Nkisi Aroli a birnin Onitsha dake jihar Anambran Najeriya ya ruguza a ranar Laraba 11 ga watan Satumba.

Gidan dai mallakin Chukwuma Njeka ne kuma mun samu rahoton cewa gidan ruguje ne a dalilin ruwan sama da a kayi kamar da bakin kwarya a safiyar Laraba.

KU KARANTA:Mutumin da ya kashe shanu 4 ya gurfana gaban kotu

Majiyar The Nation ta sanar damu cewa, duk da yake babu asarar rayuka a cikin wannan al’amari amma dai an samu asarar kadarorin da kawo yanzu ba a san adadin kudinsu ba.

Haka zalika, katangar tsohon yarin Onitsha ta fadi a sakamakon ruwan saman da aka yi da misalin karfe 6:30 na safiyar Laraba.

Babu mutum ko daya da ya jikkata a gidan yarin kuma babu ko guda daga cikin ‘yan gidan yarin da ya gudu a sanadiyar aukuwar wannan al’amari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Haruna Muhammad ya tabbar da aukuwar lamarin inda ya ce an tura da jami’ai wuraren da wannan abu ya faru domin hana ‘yan dauke-dauke da ba a rasa ba.

A wani labarin mai kama da wannan za kuji cewa, Idris Wada ya kai karar Samson Aku kotu a dalilin kashe masa shanu hudu da yayi.

Idris ya shaidawa wata kotu a Abuja cewa dansa ne ya kira shi ya fada masa yayi gaggawar zuwa gona ya duba shanunsa domin akwai wanda ya afka masu a wannan lokacin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel