Yanzu Yanzu: Ahmed Abdulrahman ya zama sabon kwamishinan yan sandan jahar Enugu
Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana sunan Ahmed Abdulrahman a matsayin sabon kwamishinan yan sandan jahar Enugu.
CP Ahmed ya kasance tsohon Kwamishinan yan sandan jahar Kaduna.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan wasu gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a wani caji, watau ofishin rundunar Yan sandan Najeriya dake Ikirike na jahar Enugu.
Idan za ku tuna Legit.ng ta ruwaito wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan sun shiga ofishin Yan sandan ne kamar za su kai musu kara, amma shigarsu ke da wuya, sai yan bindigan suka bude musu wuta.
Sai dai babu tabbacin ko akwai wanda aka kashe a sanadiyyar wannan harin, haka zalika babu tabbacin ko sun kwashe makaman dakunan.
KU KARANTA KUMA: Hotunan Buhari a kasar Japan ba na bogi bane – Bashir Ahmad
Kaakakin rundunar Yan sandan jahar Enugu, Ebere Amaraizu ya tabbatar da kai harin, amma yace babu wani mutu ko daya da aka kashe, amma yace sun kaddamar da farautar miyagun don hukuntasu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng