Wadume: Labarin mai garkuwa da mutanen da Sojoji su ka saki a Najeriya

Wadume: Labarin mai garkuwa da mutanen da Sojoji su ka saki a Najeriya

Wani Soja ne a ka zargi da laifin sakin Mai garkuwa da mutanen nan da a ka kama kwanaki watau Hamisu Wadume. Sojan ya bar Mai garkuwa da mutanen ya tsere ne bayan a da an cafke shi.

Daily Trust ta rahoto cewa wani Kyaftin din Sojin Najeriya ne ya kyale Wadume ya tsere bayan wasu ‘Yan Sanda sun cafke shi. Su kan su wadannan ‘Yan Sanda sun gamu da ajalinsu a hannun Sojojin.

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa bayan Dakarun Sojojin kasar sun harbe ‘Yan Sandan da su ka damke Wadume, bayan nan sun maida wannan gawurtaccen mai laifi har cikin gidansa a Garin Ibi.

Kyaftin din Sojan da ya yi wannan aiki ya dauki wannan mutumi da a ke zargi da laifin satar Bayin Allah zuwa Barikin Sojoji inda daga nan ya samu mai walda ya tsinka marin da a ka garkame sa da su.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin babban Sojan Najeriya Ibrahim Babangida

Wani da abin ya faru a kan idanunsa ya bayyana cewa Jami’an Sojojin kasar sun hada kai da wasu ‘Yan Sanda inda su ka rusa duk wata shaida dangane da kama wannan gawurtaccen mai garkuwa da mutane.

Majiyar ta bayyana cewa sai dai duk da wannan ta’adi da jami’an tsaro su ka yi, akwai wasu hujjojin da za su fallasa abin da ya wakana. Yanzu dai jami’an ‘Yan sanda sun yi gum game da lamarin.

A na su bangaren, Sojojin Najeriya su ma ba su bari sun ce wani abu game da batun ba, Kanal Onyema Nwachukwu wanda ke magana a madadin Sojin kasar bai ce komai ba sa'ilin da a ka tuntubesa jiya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel