Hajjin bana: Najeriya ta rasa mahajjata 9 a kasar Saudiyya
Rahotanni sun kawo cewa yawan adadin mahajjatan Najeriya wadanda suka mutu a kasa mai tsarki ya kai tara.
Dr. Ibrahim Kana, Shugaban tawagar likitoci na hukumar kula da mahajjatan Najeriya (NAHCON), ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba bayan wata yar Najeriya daga karamar hukumar Oshodi dake jihar Legas, Alhaja Folashade Lawal ta zube.
Yace a makon da ya gabata ne mahajjata uku daga Kano, biyu daga Katsina, daya daga sakoto da kuma daya daga Nasarawa tare da daya daga cikin mahajjatan kasar waje suka rasa rayukansu a hajin bana.
Kwamishinan dake kula da harkokin kiwon lafiya yace an rage yadda ake yawan tura marasa lafiya asibitocin Saudiyya face wadanda ke fama da rashin lafiya mai tsanani.
KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya ya dawo da $800 da ya tsinta a kasar Saudiyya
Yace ya fi sauki a yanzu idan mahajjata na fama da rashin lafiya, suna iya shiga runfuna ba tare da wahala ba don gabatar da matsalolinsu.
Dr Kana yace yawancin matsalolin daga marasa lafiya ya hada da ciwon jiki sakamakon tafiya mai nisa da suke yi tare da yaduwar cututtuka da ake dauka ta hanyar tari, mura da kuma matsalar da ya shafi citittukan kirji.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng