Fyade, madigo da zinace-zinace su ka haddasa mana bala’i a kasar nan – Inji Sarkin Gwandu

Fyade, madigo da zinace-zinace su ka haddasa mana bala’i a kasar nan – Inji Sarkin Gwandu

- Muhammadu Bashar ya ce sabawa Allah ne ya jawo matsalar rashin tsaro a fadin Najeriya

- Sarkin Gwandu ya ce zina da madigo da fyade su ka haddasa satar mutane da a ke yi a yau

- Mai Martaban ya ce ba za a daina hallaka jama’a ba har sai mutane sun koma ga Ubangiji

Mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Bashar, ya daura laifin sace-sace da garkuwa da mutane da a ke yi a Najeriya a kan yadda mutane su ke sabawa Ubangiji da biyewa rudun shaidan.

Sarkin na kasar Gwandu ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya ke yi wa jama’ansa magana bayan kammala sallar babbar idi a Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta a Garin Gwandu da ke cikin jihar Kebbi.

KU KARANTA: Gwamna Tambuwal ya yi kira ga mutane su sa kasa a cikin addu'a

Mai martaba Sarkin ya ke cewa: “Al’ummar mu ta yau cike ta ke da matsalolin fyade, da madigo da kuma bin maza, wanda wadannan duk su ka kawo mana matsalolin rashin tsaro da a ke ciki Najeriya.”

Sarkin ya ke cewa jama’a sun bar Allah don haka su ke fama da halin rashin tsaro. Shugaban Sarakunan na jihar Kebbi ya ke cewa muddin jama’a ba za su tuba ba, ba za a ga karshen wannan bala’i ba.

Sarkin ya ce: “Neman Duniya ko ta wani irin hali da kuma rashin da’a ne ya jefa mu cikin yanayin da mu ka samu a ciki.” Sarkin ya nemi mutane su komawa Ubangiji, sannan ya ce su zama masu tausayi.

Alhaji Bashar ya ja hankalin wadanda su ka samu damar yin layya su taimakawa wadanda Ubangiji bai ba ikon yanka dabba a lokacin wannan biki na sallah ba. Sarkin ya yi wa kasa baki daya addu’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng