Asarar haihuwa: Wani mutumi dan shekara 40 ya halaka babansa a jahar Neja

Asarar haihuwa: Wani mutumi dan shekara 40 ya halaka babansa a jahar Neja

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Minna na jahar Neja ta bada umarnin garkame wani mutumi dan shekara 40, Bisso Aminu da aka gurfanar dashi gabanta kan tuhumarsa da kashe mahaifinsa.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Alkalin kotn, Binta Rijau ta umarci a daure mata Bisso ne har sai ta samu shawara daga bakin babban jami’I mai shigar da kara na jahar Neja a kan sharia’ar.

KU KARANTA: Kalli wani Alhaji yana dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa

Da farkon zaman, Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Thomas Peter ya bayyana ma kotun cewa dakacin kauyen Tangu dake cikin karamar hukumar Rijau ne ya kai kara zuwa ofishin Yansanda a ranar 24 ga watan Yuli.

Dansandan yace Bisso Aminu ya kashe mahaifinsa ne a kan zarginsa da maita, kuma ya yi zargin mahaifin nasa na kokarin kasheshi ne, don haka shi ya riga kasheshi ta hanyar makeshi da fartanya yayin da yake barci.

A wani labarin kuma, yansanda sun gurfanar da wani matashi dan shekara 25, mai suna Sunday John gaban wata kotun majistri kan zarginsa da lakadama ma uwarsa Virginia John dan banzan duka da gora, a jahar Ondo.

Sunday ya casa mahaifiyarsa da gora ne har sai da ta fadi sumammiya, sa’annan ya targadata a wurare daban daban tare da ji mata raunuka da dama a jikinta.

Dansanda mai shigar da kara, Abiodun Adebiyi ya shaida ma kotu cewa suna tuhumar Sunday da aikata laifuka uku da suka danganci cin zarafi, barazana ga rayuwa da kuma barazanar tayar da hankulan jama’a.

Sunday ya amsa laifukansa, sa’annan kotun ta dage cigaba da sauraron karar kamar yadda Dansanda mai shigar da kara ya bukata domin gudanar da bincike tare da yin nazari a kan sharia’ar, sa’annan kotu bada umarnin a garkame Sunday a kurkuku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel