Asiri ya tonu: Maigadi da wasu mambobin coci sun hada baki sun sace naira miliyan uku daga cikin akwatin neman taimako ta coci

Asiri ya tonu: Maigadi da wasu mambobin coci sun hada baki sun sace naira miliyan uku daga cikin akwatin neman taimako ta coci

- An gurfanar da wasu mutane da suka yiwa akwatin neman taimako ta wata coci karkaf

- Mutanen sun sace kudi kimanin naira miliyan biyu da dubu dari bakwai a cikin akwatin neman taimakon

- An bayyana cewa daya daga cikin masu laifin mai gadin cocin ne, yayin da sauran kuma suke mambobi na cocin

Jami'an hukumar 'yan sanda sun gurfanar da wasu mutane biyu, Osita Egbo da Joel Okafor a gaban Kotun Majistire ta jihar Legas da take zaune a unguwar Yaba, da laifin sace kudi kimanin naira miliyan biyu da digo bakwai daga cikin akwatin neman taimako ta coci.

An ruwaito cewa a ranar 2 ga watan Yuli, 2019, mutanen da ake tuhuma din sun sace naira miliyan 2.7 daga cikin akwatin neman taimako ta cocin Mountain of Fire and Miracles dake yankin Onike cikin unguwar Yaba dake jihar Legas.

KU KARANTA: Mata sun koma yiwa maza fyade: An kwaci wani mutumi dakyar a hannun wata mata da take kokarin yi masa fyade

An ruwaito cewa Egbo mai gadi ne a cocin yayin da shi kuma Okafor yake mamba na cocin. A cewar mai gabatar da kara, Modupe Olaluwoye, masu laifin sun sace kudin daga cikin akwatin da ake tara kudin taimako na cocin.

Mai gabatar da karar ya bayyana cewa daya daga cikin masu laifin wanda yake ganin kamar an cuce shi ya amsa laifinsu.

Alkalin kotun mai shari'a Oluwatoyin Ogere, ta bayyana cewa ta bayar da belin masu laifin akan kudi naira miliyan daya kowanne sannan da shaidu guda biyu.

Sannan a karshe ta daga sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Satumbar wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel