Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul aziz Yari ya ce yin sulhu da yan ta'adda ba zai haifar da 'da mai ido ba

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul aziz Yari ya ce yin sulhu da yan ta'adda ba zai haifar da 'da mai ido ba

-Bello Matawalle ya bayyana cewa saban tsarin yin sulhu da yan ta'addan Zamfara da gwamnatinshi ta shigo da shi na haifar da sakamako mai kyau

-Tsohon gwamnan jihar Abdul-Aziz, ya bayyana cewa durkusar da yan ta'adda da karfi ne kadai hanyar da za a samu saukin ta'addanci a jihar

-Yari ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa ya yi sulhu da yan ta'adda har sau biyu amma hakan bai hanasu cigaba da kashe kashe da sace sacen mutane ba

A satin da ya gabata, gwamna Bello Matawalle ya bayyana cewa saban tsarin yin sulhu da yan ta'addan Zamfara da gwamnatinshi ta shigo da shi na haifar da sakamako mai kyau kasancewar an shafe sati uku ba a samu rahoton harin yan ta'adda ba wanda hakan ne karo na farko tun shekaru hudu da suka wuce.

Amma tsohon gwamnan jihar Abdul-Aziz Yari wanda ake zargin al'amurran tsaro sun tabarbare a zamanin mulkinsa, ya bayyana cewa durkusar da yan ta'adda da karfi ne kadai hanyar da za a samu saukin ta'addanci a jihar.

Tsohon gwamnan ya ce ko a lokacin mulkinsa ya dauki matakai na yi wa 'yan ta'adda afuwa, inda ya ce lokacinsa an kubutar da mutane, a sulhun da aka yi da Buharin Daji.

KARANTA WANNAN: Harin ‘Yan bindiga ya sa mutanen Kauren-Namado sun yi zanga-zanga

Ya ce : "Nayi sulhu da yan ta'adda sau biyu amma a karo na uku na ce ba zan sake ba saboda hakan bai hana sata da kashe kashen mutane da dabbobi da ake yi a Zamfara ba"

"Dole idan za ka yi sulhu to sai bangare daya da nuna fin karfi ya nuna cewa na fi karfin ka dole ka mika wuya," in ji Yari.

Gwamna Matawalle ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu a shirinsa na yin sulhu da yan ta'adda, inda ya kara da cewa tun da farko ba a bi hanyoyin da suka dace ba.

Ya ce a dalilin sulhu da yan ta'addan sun sako mutane 335 ba tare da an biya wani kudin fansa ba. ya ce: "Mun ja layi cewa kowa ya ajiye makansa sa'annan kada wani bangare ya dorawa dayan laifi."

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel